Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Corronavirus:ta kashe mutum 12 Nigeria,wasu 1,544 sun kamu ranar jumma,a

Bincike daga hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta nuna cewa a ranar Juma'a, an samu ƙarin mutum 1,544 da suka kamu da cutar korona a ƙasar.

ASALIN HOTON,NCDC


Ƙididdiga daga hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta nuna cewa a ranar Juma'a, an samu ƙarin mutum 1,544 da suka kamu da cutar korona a ƙasar.


A cewar bayanin da NCDC ta wallafa a shafinta na Tuwita, cikin sa'a 24 da ta gabata, mutum 12 ne cutar ta yi ajalinsu sannan mutum 411 sun warke har an sallame su daga asibiti.


Har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana ɗayan inda take da mutum 739 sai kuma jihar Plateau da ke biye da ita da mutum 168.


Ita kuwa Abuja babban birnin kasar na da mutum 153 da suka kamu da cutar sai kuma jihar Oyo-91, Nasarawa-90, Rivers-80, Kaduna-35, Edo-33 , Kano-29 da jihar Ogun-21.


Jihohin da ke da kasa da mutum 20 su ne Delta-19 da Sokoto-16 da Akwa Ibom-11 da Ebonyi-11 da Enugu-10 da kuma Osun-10.


Sauran masu kasa mutum 10 su ne Niger-9, Bauchi-8, Kebbi-8, Katsina-2 da kuma Taraba-1.


A Najeriya dai, gaba ɗaya mutanen da suka kamu da korona ya zuwa ranar Juma'a ɗin, sun kai 97,478 sannan an sallami mutum 78,552 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga cutar kuma mutum 1,342 ne suka mutu tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.



Coronavirus: Taswirar da ke nuna yawan wadanda suka kamu a duniya

Adadin masu coronavirus a kasashen Afrika

Coronavirus: Abubuwan da ya kamata ku dinga yi

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.


Ta Yaya zan kare kaina daga cutar?


Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:


■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta


■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.


■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.


■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Post a Comment

0 Comments