A Nigeriya hukumar hana manyan laifuka, wato fasa kwauri, ta dora wa jama'ar kasar laifi, cewa ba sa bayar da gudunmawar da ta dace domin yaki da miyagun kwayoyi musamman Tramadol da Coden da ake shigo da su kasar daga waje.
Hukumar kwastam din ta ce tana samun nasarar dakatar da shigowar wadannan kwayoyin, to amma al'umma na yin kauron baki, wajen fallasa masu amfani da wadanann kwayoyi.
To amma ta ce tana zargin cewa suna hakan ne da tsoron cewa idan su ka tona za a iya hallaka su, ko kuma masu shan kwayoyin yan uwansu ne.
Babban jami'in kwastam mai kula da shiyyar gabar teku ta Apapa da ke Legas Muhammad Abba Kura, ya fada wa BBC cewa rufa wa ire-iren wadannan mutane asiri ba karamin hadari ba ne ga iyali da kuma al'ummar kasar.
A cewarsa daga watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekarar kawai sun kama kwantenoni 328, kuma 72 daga cikinsu su na dauke ne da irin wadannan magunguna da gwamnati ta haramta amfani da su kwata kwata.
'Daga cikin su akwai Tramadol, akwai magungunan tari irinsu Coden, wanda tun da dadewa gwamnati ta hana shigowa da shi'.
'Wannan shine ma babban dalilin da ya sa mu ka kwace kwantenar saboda tana dauke da Coden'.
Jami'in ya Kara dacewa
'Ban da ma akwai Coden, maganin ba shi da rajista, babu kwanan wata da shekara a jikinsa, kuma ba a rubuta kasar da a ka samar dashi ba.'
Akan haka jam'in ya nemi al'umma da su taimaka wa hukumomi wurin tona asirin irin wadannan bata gari ko da kuwa yan uwansu ne.
Duk da Mr Kura bai musanta a na hada baki da jam'ian hukumar ba wurin aikata miyagun laifuka, ya ce a ko da yaushe suna bullo da hanyoyin lalata shirin bata gari daga cikin su.
0 Comments